Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kabiru Bashiru: Cutar COVID-19 ba ta kawo cikas ga zaman rayuwata ba
2020-03-03 09:57:33        cri


Yayin da kasar Sin ke ci gaba da himmatuwa wajen ganin bayan annobar cutar numfashi ta COVID-19, wakilin sashin Hausa na CRI Murtala Zhang ya zanta da wasu daliban Najeriya da a yanzu haka suke kasar, domin jin ra'ayoyinsu kan matakan dakile cutar.

Kabiru Bashiru, dan jihar Kanon tarayyar Najeriya ne wanda ke karatun digiri na biyu a fannin kimiyya da fasahar harkokin sufurin jiragen ruwa dake jami'ar Ningbo a lardin Zhejiang. A zantawarsa da Murtala Zhang, Malam Kabiru Bashiru ya ce, da farko yana ganin an takura su ne saboda an ayyana dokar hana shiga da fita a makaranta, amma daga baya ya fahimci cewa, wannan mataki da aka dauka ya dace matuka, saboda yana taimakawa sosai wajen ganin bayan cutar, haka kuma ya ce, cutar ba ta kawo cikas ga zaman rayuwarsa a makaranta ba, saboda yana iya sayen kome ta kafar sadarwar intanet.

Ga dai yadda hirar tasu ta kasance.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China