Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: An kaddamar da gangamin kasa domin yaki da zazzabin Lassa
2020-03-02 11:27:50        cri
A jiya Lahadi ne gwamnatin Najeriya, ta kaddamar da gangamin kasa baki daya, game da yaki da cutar zazzabin Lassa, wadda daga farkon shekara kawo yanzu ta hallaka mutane sama da 100.

Yayin kaddamar da gangamin, ministan ma'aikatar muhallin kasar Mohammad Abubakar, ya yi kira ga al'ummar kasar da su kare gidajen su daga beraye, da sauran dabbobi masu nasaba, kasancewar su ne ke yada cutar tsakanin al'umma, musamman ma a wurare masu rangwamen tsafta.

Ministan ya kara da cewa, ma'aikatar sa za ta tabbatar da tsaftar muhallan al'umma, kasancewar hakan shi ne mataki mafi alfanu, na dakile yaduwar wannan cuta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China