Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin nune-nunen nasarorin wasanni na Sin domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin
2019-09-12 14:21:53        cri

An yi bikin nune-nunen nasarorin wasanni na Sin, domin murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin a birnin Taiyuan dake lardin Shanxi na kasar Sin. Shugaban hukumar harkokin wasanni ta kasar Sin Gou Zhongwen, da mataimakin shugaban lardin Shanxi Zhang Fuming, da mataimakin hukumar harkokin wasanni ta kasar Sin Li Jianming, da sauran jami'an harkokin wasanni sun halarci bikin budewar.

A cikin jawabinsa, Mr Li Jianming ya bayyana cewa, taken bikin a wannan karo shi ne "bunkasa sha'anin wasanni, da kuma bunkasa kasar Sin". A gun bikin, an yi amfani da hanyoyin gwada hotuna, da kayayyaki, da bidiyo, da tambaya da amsa da sauransu, wajen waiwayen ayyukan raya wasanni a cikin shekaru 70 bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, da gwada nasarorin da Sin ta samu, da labaran wasanni na Sin masu burge jama'a, da yada tunanin wasanni da al'adun wasanni na Sin.

A cikin shekaru 70 da suka gabata, Sin ta bi tunanin bunkasa wasanni domin jama'a, ta samu nasarori da dama, wadanda suka burge dukkan duniya sosai. Sha'anin wasanni ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar jikin jama'a, da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma, da raya al'adu, da kuma yin mu'amala da juna a tsakanin kasa da kasa a fannin al'adu da dai sauransu.

Mataimakin shugaban lardin Shanxi Zhang Fuming ya bayyana cewa, bikin ya shafi gwada nasarorin da Sin ta samu a fannin wasanni a cikin shekaru 70 bayan kafuwar sabuwar kasar Sin. Yayin da jama'a suke kallon hotuna, ko bidiyo, ko kayayyaki na zakarun wasanni kasar Sin, ana iya waiwayar lokutan Sin na nasara a fannin wasanni, da kuma nuna yabo ga 'yan wasan kasar.

An ce, an gwada kayayyaki 143, da hotuna 252, da bayanai masu kalmomi fiye da 6800 a gun bikin nuna-nunen. An kuma kasa bikin kashi shida, wato "jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin", da "tutar kasar Sin", da "tunanin wasanni", da "wasannin motsa jiki a tsakanin jama'a", da "harkokin waje a fannin wasanni", da kuma "bunkasa kasa, sai kuma bunkasa wasanni".

Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin, ta cimma nasara a wasanni sau da dama. A shekarar 1984, Xu Haifeng ya cimma nasarar samun lambar yabo ta zinari ta farko ta kasar Sin a tarihin wasannin Olympics, a gun gasar wasannin Olympics ta Los Angeles. A shekarar 1981, kungiyar wasan kwallon raga mata ta kasar Sin ta zama zakarar duniya karo na farko, wadannan duk sun alamta ewa, Sin na kokarin inganta karfin wasanni, da kuma bayyana cewa, Sin ta samu ci gaba a fannin wasanni. Ya zuwa karshen shekarar 2018, 'yan wasan kasar Sin sun cimma nasarar zama zakarun duniya har sau 3458, da samun lambobin yabo na zinari na wasannin Olympics 237, da kuma karya bajimtar duniya sau 1332.

Game da tarihin wasannin lokacin hunkuru kuwa, 'yan wasan kasar Sin a wannan fanni sun kiyaye yin kokarin neman cimma burinsu, wadanda suka shaida tunanin wasanni na kasar Sin na kiyaye yin kokari sosai.

Ban da wasannin motsa jiki, an raya sha'anin wasannin motsa jiki a tsakanin jama'a, da harkokin waje a wannan fanni. A cikin shekarun 70, jami'oin wasanni na kasar Sin sun bada ilmi, da horar da kwararru, da masu nazari a fannin wasanni. Karin kwararru a fannin wasanni sun kara taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga raya sha'anin wasannin motsa jiki a tsakanin jama'a, da inganta fasahohin wasanni.

Sha'anin wasanni ya alamta bunkasuwar zamantakewar al'umma da dan Adam, kana yana shaida karfin wata kasa da al'adunta. Idan karfin kasar Sin ya bunkasa, shi ma sha'anin wasanni na kasar ya bunkasa. A cikin shekarun 70, an ajiye abubuwa da dama game da bunkasuwar sha'anin wasanni na kasar Sin, wadanda suka shaida tarihin inganta sha'anin wasanni na sabuwar kasar Sin. Masu aikin wasanni na kasar Sin sun yi imanin cewa, za su yi kokarin cimma burin bunkasa wasanni mai karfi a kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China