Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta yi alkawarin bunkasa zuba jari a kasuwar hannayen jarin kasar
2020-02-26 09:33:59        cri
Ministar harkokin kudi, kasafi da tsare-tsare ta Najeriya, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa, gwamnati ta yi alkawarin kara bullo da matakan da za su bunkasa zuba jari a kasuwar hannayen jarin kasar.

Ministar ta bayyana haka ne yayin da ta ziyarci hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriya (NSE) dake Lagos. Ta ce, a baya gwamnati ta hada kai da hukumar ta NSE a fannoni daban-daban, don tabbatar da bunkasa da ci gaban kasuwar.

Ministar ta kara da cewa, wasu tanade-tanaden haraji da aka bullo da su karkashin kudurin dokar harkokin kudi ta shekarar 2019, za su taimaka wajen kara zurfafa kasuwar a fannoni zuba jari, da shirye-shiryen rukunin gidajen kwana, da ba da rancen takardun lamuni.

Ta kuma baiwa masu hada-hadar hannayen jari tabbacin cewa, dokar da ake shirin kafawa, za ta tanadi wasu tallafi da za su kara janyo masu sha'awar zuba jari a kasuwar.

Ministar ta kuma ce, dokar harkokin kudi ta shekarar 2019, ta yi la'akari da wasu matakai na tallafi, tana mai cewa, wajibi ne duk wani kudirin doka da za a gabatar game da harkokin kudi a ko wace shekara, ta kunshi tanadi na samar da tallafi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China