Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Rasha za ta daidaita matakinta na hana Sinawa shiga cikin kasarta
2020-02-19 20:37:39        cri

A kokarin da ake yi na shawo kan hadarin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, Rasha ta sanar da cewa, tun daga ranar 20 ga watan nan, za ta hana wasu Sinawa shiga cikin kasarta na dan wani lokaci. Game da batun, Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya bayyana cewa, tuni Rasha ta sanar da Sin daukar wannan mataki ta kafofi na diflomasiya. Kuma Sin na fatan gami da imanin cewa, kasashen duniya ciki har da Rasha za su kalli yanayin annobar da Sin ke ciki da idon basira, kuma ana sa ran za ta daidaita matakin ba tare da bata lokaci ba, domin tabbatar da cudanya da hadin gwiwar bangarorin biyu.

Geng ya ce, Rasha ta jaddada cewa, tana da imanin cewa, Sin za ta cimma nasarar yaki da cutar, amma ta dauki wasu matakan kayyadewa na wucin gadi ne domin dakile yaduwar cutar. Amma matakin ba ya nufin cewa, za a hana cudanyar jama'ar kasashen biyu daga dukkan fannoni, muddin yanayin cutar ya inganta, to za a daidaita ko kuma soke matakin. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China