Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun kashe a kalla mutane 6 a arewacin Najeriya
2020-01-16 08:59:00        cri

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa, a kalla mutane 6 ne suka gamu da ajalinsu, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kaddamar da hari kan ayarin sarkin Pokiskum Umaru Bubaram a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria dake yankin arewacin kasar a daren ranar Talata.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kaduba Yakubu Sabo, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hudu daga cikin wadanda aka kashen dogaran sarkin ne, kana sauran biyu wasu matafiya ne. Haka kuma sarki Umaru Bubaram ya samu rauni, amma yana murmurewa a wani asibitin yankin da ake kula da shi.

Rahotanni na cewa, an ga motoci babu kowa a ciki, lokacin da 'yan sanda suka iso wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuna cewa, da alamun 'yan bindigar sun yi awon gaba da mutane da dama.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China