Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko fasahar 5G ta kamfanin Huawei za ta kawo barazana ga tsarin demokradiyya?
2020-02-16 17:09:52        cri

A ranar 14 ga wata, shugabar majalisar wakilai ta kasar Amurka Nancy Patricia D'Alesandro Pelosi ta yi jawabi a taron kiyaye tsaro na Munich cewa, ya kamata kasa da kasa su yi watsi da kamfanin fasaha na Huawei na kasar Sin yayin da suke raya tsarin internet na fasahar 5G. A cewarta, Sin tana yunkurin raya tsarinta na fasahar sadarwa ta hanyar kamfanin Huawei don kawo barazana ga kasashen da ba su yin amfani da fasahar.

Mataimakiyar direktan kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin kuma tsohuwar mataimakiyar ministan harkokin wajen kasar Sin Fu Ying ta mayar da martani da Turanci nan da nan, inda ta yi nuni da cewa, bayan da Sin ta bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima, an shigar da fasahohin kasashen yammacin duniya iri daban daban, amma ba a kawo barazana ga tsarin siyasa na kasar Sin ko kadan ba. Fu Ying ta gabatar da tambaya ga Pelosi cewa, mene ne dalilin da ya sa idan aka shigar da fasahar kamfanin Huawei don raya fasahar 5G a kasashen yammacin duniya, wace irin barazana ce zai kawo ga tsarin siyasar tasu? Ko Pelosi ta yi tsammani tsarin demokuradiyyar ba shi da inganci ne, shin wace barazana kamfanin fasaha kamar Huawei zai kawo gare su? Bayan da Fu Ying ta bayyana hakan, masu kallo a wurin sun yi tafi da nuna amincewa gare ta sosai. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China