Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei ya kaddamar da ranar kirkire-kirkire ta arewacin Afirka a Tunisiya
2019-09-24 09:49:03        cri

Jiya ne kamfanin sadarwa na kasar Sin, Huawei tare da hadin gwiwar gwamnatin Tunisiya, ya kaddamar da wani dandali game da ranar kirkire-kirkire ta arewacin Afirka a kasar Tunisiya.

A jawabinsa na bude dandalin, mataimakin shugaban rukunin kamfanin Huawei Xue Man, ya bayyana cewa, muddin aka hada kai wajen inganta kayayyakin more rayuwar jama'a, babu shakka za a yi nasarar gina managarcin tsarin fasahar kere-kere a Tunisiya da yankin kasashen Larabawa da ma nahiyar Afirka baki daya.

Ya kuma bayyana kudirin kamfanin Huawei na samar da dukkan taimakon da ya dace na cimma wannan manufa. Shi ma a nasa jawabin, ministan sadarwa da harkokin cinikayya ta yanar gizo na kasar Tunisiya, Mohamed Anour Maarouf, bitar makomar fasahar sadarwa ya yi a kasar Tunisiya, yana mai yaba hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kamfanin na Huawei.

Sama da jami'ai da masana 300 daga kasashen Larabawa da Afirka ne suka halarci taron. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China