Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da jita-jitar da ake yadawa game da rikicin tsaron 5G na Huawei
2019-09-16 20:13:08        cri

A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan matsayinta na yin adawa da jita-jitar da ake yadawa, game rikicin tsaro na fasahar 5G ta kamfanin Huawei, haka kuma tana adawa da matakin da aka dauka bisa dalilin tsaron kasa, domin hana ci gaban fasahar sadarwa ta kamfanonin kasar Sin.

A ranar 12 ga wata, jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Robert Strayer ya bayyana cewa, ya tattauna da shugaban kwamitin sadarwa na tarayyar Amurka, yayin da suke ziyarar kasashen Saudiya, da Daular Labarawa, da Bahrain, kan batun da ya shafi rikicin tsaro na fasahar 5G ta kamfanin Huawei, inda suka bayyana cewa, idan Amurka tana son tabbatar da tsaron yanar gizonta, to ya zama wajibi a hana kamfanin Huawei amfani da fasahar 5G.

Kan wannan, Hua ta yi nuni da cewa, a cikin 'yan watannin da suka gabata, ba ma kawai Amurka ta danne wasu kamfanonin kasar Sin ba, har ma ta yada jita-jita a fadin duniya, domin shafawa kasar Sin kashin kaji, kana matakin da Amurka ta dauka ya sabawa ka'idojin kasa da kasa, haka kuma babu mutunci ko kuma kunya a cikin sa.

Ta ce hakika jita-jitar da Amurka ta yada game da rikicin tsaron fasahar 5G ba shi da tushe ko kadan, kuma babu sharadi da ya nuna cewa, fasahar 5G tana kawo kalubale ga tsaron wata kasa, ko hukuma, ko kungiya ko wani mutum. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China