Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan bindiga sun kashe mutane 14 a arewacin Nijeriya
2020-01-18 17:00:04        cri
Mutane akalla 14 sun mutu, sanadiyyar farwa kauyensu da wasu 'yan bindiga suka yi, a jihar Zamfara dake arewacin Nijeriya.

Kakakin 'yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya bayyana cewa, baya ga wadanda suka mutu, akwai wasu mutanen da suka jikkata da ba a san adadinsu ba, sanadiyyar harin da aka kai kauyen Babban Rafi na yankin Karamar Hukumar Gummi ta jihar.

Ana zargin maharan da ba a san ainihin manufarsu ba, sun shiga kauyen ne daga jihar Kebbi dake makwabtaka da yankin.

Majiyoyi a yankin sun ce 'yan bidagar sun shiga kauyen ne a kan babura fiye da 40, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi. Sun kuma kwashe dabbobi da wasu dukiyoyin mutanen kauyen. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China