Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Liberia ta ayyana dokar ta baci a fannin kiwon lafiya bayan cutar Lassa ta kashe mutane 21
2019-09-03 12:51:58        cri
A jiya Litinin hukumomin lafiyar kasar Liberia sun sanar da ayyana dokar ta baci bayan barkewar annobar zazzabin Lassa wanda kawo yanzu yayi sanadiyyar hallaka rayukan mutane 21 a cikin wannan shekarar.

Babban jami'in kiwon lafiyar kasar Liberia Francis Kateh, ya fadawa manema labarai cewa kawo yanzu, an samu yankuna 4 da aka samu yaduwar kwayar cutar.

Kateh yace, babban abin damuwa shine, ma'aikatan lafiya wadanda suke da kwarewar aikin ganowa cutar tare da bada kulawa ga wadanda suka kamu da cutar, su kansu suka kamu, to hakika al'amarin cutar ya ta'azzara kenan.

Yace an samu wani jami'an dake aiki a dakin gwaje gwaje wanda aka tabbatar yana daya daga cikin mutanen da cutar ta hallaka tsakanin watan Janairu zuwa 25 ga watan Agusta.

Babban daraktan cibiyar kula da lafiya ta kasar Tolbert Nyenswah, ya ayyana cutar a matsayin Ebola kashi na biyu, ya bukaci a dauki tsauraran matakan dakile cutar.

Nyenswah ya bayyana cewa, "Zazzabin Lassa Ebola ce ta biyu, babu bukatar boye wani bayani. Ya kamata mu fitar da bayanin a fili game da halin da muke ciki, da kuma yadda zamu yi riga kafin cutar".

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China