2019-06-01 15:37:59 cri |
An tattara alkaluman ne tun daga farkon shekarar nan, daga jihohi 21 da kawo yanzu cutar ta shafa a kasar dake yammacin Afrika.
Ya zuwa watan Afrilu, jimilar mutane 121 ne suka mutu tun bayan barkewar cutar a ranar 13 ga watan Junairu.
Cikin wata sanarwa da aka fitar, shugaban hukumar takaita yaduwar cutaka ta kasar, Chikwe Ihekweazu, ya ce ya zuwa ranar 26 ga watan Mayu, an tabbatar da mutane 578 ne suka kamu da cutar.
A ranar 22 ga watan Junairun bana ne kasar ta tabbatar da barkewar cutar, inda ma'aikatan lafiya 17 daga jihohi 7 na kasar ke cikin wadanda suka kamu da ita. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China