Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jagororin JKS sun tattauna game da yanayin da ake ciki game da cutar numfashi
2020-01-25 20:51:12        cri
Zaunannen ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS, ya yi zama a ranar Asabar, inda mambobin sa suka tattauna game da yanayin da ake ciki don gane da ayyukan kandagarki, da magance cutar numfashin nan ta coronavirus da ta bulla a sassan kasar.

Shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin Xi Jinping ne ya jagoranci zaman na yau Asabar. Zaman taron ya kuma amince da kafa tawagar musamman daga kwamitin kolin JKS, domin jagorantar ayyukan sa ido na dakile wannan cuta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China