Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: Sin na nuna daidaito ga kamfanoni masu salo daban-daban
2019-12-24 13:29:43        cri

Da safiyar yau Talata, firaministan kasar Sin Li Keqiang da shugaban kasar Koriya ta kudu Moon Jae-in, da kuma takwaransa na Japan Abe Shinzo sun halarci taron koli na masana'antu, da kasuwanci na kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu karo na 7 a birnin Chengdu na lardin Sichuan, inda Li Keqiang ya bayyana cewa, ban da bude kofa kan sana'ar kere-kere, Sin za ta kara bude kofarta kan sana'ar ba da hidima, da ba da izini ga karin sana'o'i masu dogaro da jarin ketare, da kuma samar da yanayin takara bisa tsarin kasuwa cikin adalci.

Ya kara da cewa, Sin za ta nace ga manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa a waje, ba za ta kuma nuna bambanci kan kamfanoni masu salo irin daban-daban ba. Kaza lika za ta yi iyakacin kokari, wajen yaki da laifin keta ikon mallakar ilmi. Ya ce Sin na fatan kara hadin kai da kasashen Japan da Koriya ta kudu, don koyi da juna da cin moriya tare. Li ya kara da cewa, habaka bude kofa wani zarafi ne mai kyau ga kamfanonin kasashen biyu wato Japan da Koriya ta kudu, don neman amfanin juna da cin moriya tare.

A nasu bangare, shugabanin kasashen biyu, sun bayyana fatan su na kara hadin kai da kasar Sin, don dukufa kan aiwatar da manufar yin ciniki maras shinge, da rage kangiyar cinikayya, da samarwa juna wani yanayi mai adalci da daidaito. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China