Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tsaurara matakan kandagarki a fannin sufuri
2020-01-25 16:26:17        cri
Sakamakon bullar cutar numfashi a sassan kasar Sin, yanzu haka mahukuntan kasar sun fara aiwatar da tsauraran matakan kandagarkin yaduwar cutar a fannin sufuri. Karkashin wannan mataki, duk wanda aka yi hasashen yana dauke da cutar, za a gaggauta kebe shi, a kuma garzaya da shi cibiyoyin lura da masu dauke da cutar, domin samun cikakkiyar kulawa.

Hukumar lafiyar kasar ce dai ta ba da umarnin daukar wannan matakin. Cikin takardar umarnin, hukumar ta umarnci masu ababen hawa da su rika gudanar da matakan tsaftace ababen hawan su, ta hanyar samar da iska mai tsafta, da sanya sinadaran kashe kwayoyin cuta. Kaza kila a duk lokacin da aka yi zargi, ko aka tabbatar wani fasinja na dauke da cutar, ko dai a jirgin kasa, ko Bas, ko jirgin ruwa ko na sama, sai a yi hanzarin mika shi ga cibiyar lura da masu dauke da cutar cikin gaggawa.

A daya hannun kuma, an umarci kananan hukumomi da su kafa cibiyoyin tantance yanayin fasinjoji a tashoshin shiga Bas, da filayen jiragen kasa da na sama da na ruwa, kana su tabbatar da sun karbi duk wani dake dauke da cutar, domin samun kulawar jami'an lafiya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China