![]() |
|
2020-01-23 20:20:10 cri |
Shirye-shiryen sun kunshi wasannin kwaikwayon ban dariya gami da raye-raye da kade-kade da wasan dabo da wasan Kungfu da sauransu.
Yawan wasannin kwaikwayon ban dariya ya kai 8 a wannan shekara, wadanda ke shafar zaman rayuwar al'umma na yau da kullum kuma masu fadakarwa da ilmantarwa. Wasannin kade-kade da raye-raye ma da za'a gabatar za su nuna yadda al'ummar kasar Sin ke nuna jajircewa ga zaman rayuwa da ayyukansu.
Har wa yau, wasan dabo da wasan lankwasa jiki wato acrobatics a turance da wasan Kungfu da sauransu za su bayyana tarihi da al'adun gargajiya da kyawawan halayen al'ummar kasar.
CMG zai gabatar da kasaitaccen bikin murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin na bana a Beijing, fadar mulkin kasar, sa'annan kuma akwai reshensa guda biyu, wadanda suka hada da babban yankin lardin Guangdong da Hong Kong da Macao da kuma birnin Zhengzhou na lardin Henan.
Mutane biyar ne za su jagoranci bikin na gobe a Beijing wadanda za su biya bukatun masu kallo sosai.(Murtala Zhang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China