Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
DAVOS na fatan saurari murya daga kasar Sin
2020-01-23 16:01:11        cri

Ana kira taron shekara-shekara na DAVOS na 2020 daga ran 21 zuwa 24 mai jigon "Hadin kan duniya don samun ci gaba mai dorewa". Ana sa ran saurari murya daga kasar Sin.

Mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng wanda ya halarci taron ya nuna cewa, hanya da ta dace da za a bi wajen magance wahalhalu da matsaloli da ake fuskantar a fuskar dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya ita ce, kafa tsarin duniya mai bude kofa da yin hakuri da juna, abin mafi muhimmanci shi ne, nace ga gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban. An ce, wannan hanya ta kasance mataki dake bayyana ruhin jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi a taron shekaru 3 da suka gabata, kuma ya bayyana cewa, Sin na yi tunani da nazari mai zurfi kan sauye-sauyen halin duniya, dake da ma'ana sosai. Sin ta yi kira ga kasashen daban-daban da su nacewa ga yin sulhuntawa cikin adalci, da taimakawa juna da hadin gwiwa don tinkarar kalubaloli tare, ta yadda za a ingiza tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya da ya kan hanya kara bude kofa da yin hakuri da juna da amfanawa kowa da samun daidaito da cin moriyar tare, ta yadda jama'ar kasa da kasa za su more ci gaban dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya da bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Wannan dai shawarar Sin ga duniya, kuma ka'ida da Sin ta dade tana aiwatarwa. (Mai fassarawa: Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China