Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da ba da jagoranci ga dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya
2020-01-21 11:20:48        cri

Za a kira taron shekara-shekara na Davos na shekarar 2020 a Switzerland. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi jawabi a gun taron Davos da aka yi shekaru uku da suka gabata cewa, an maida tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya a matsayin dalili daya tilo dake shafar matsalolin da suke dabaibaye duniya, babu tushe kuma ba shi da amfani ko kadan wajen warware matsalolin da ake fuskanta. Ya ce, don ganin zarafi da kalubalolin da ake fuskanta yayin da ake kokarin dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, ya kamata a yi amfani da duk wani zarafi da hadin kai don tinkarar dukkanin kalubale, ta yadda za a ba da jagoranci ga wannan aiki bisa matakan da suka dace.

A cikin wadannan shekaru 3 da suka gabata, Sin tana hada kai da abokanta don kiyaye wannan tsari, da ba da jagoranci ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya, ba ma kawai Sin ta ci gajiya daga wannan tsarin ba, har ma ta ba da babbar gudunmawa a wannan fanni.

Ya kara da cewa, Sin tana zurfafa bude kofa da yin kwaskwarima, kuma tana more zarafi da muradunta, da neman amfanawa juna da cin moriya tare. Sin tana kokarin hadin kan kasa da kasa ta raya shawarar "ziri daya da hanya daya" da gudanar da bikin baje kolin kasa da kasa da dai sauransu. Ban da wannan kuma, "aikin kirkire-kirkire" na kasar Sin na samarwa duniya babban karfin samun bunkasuwa. Dadin dadawa, Sin na kokarin shiga tsarin daidaita duniya da kuma yin bakin kokarinta wajen sa kaimi ga kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai adalci da daidaito. Ya zuwa yanzu, bankin raya manyan ababen more rayuwa na Asiya da Sin ta ba da shawarar gina shi ya samu mambobi 102, inda kasashe masu tasowa suka mallaki yawancin hannun jarin, lamarin da ya ba su karfin yin magana a cikin wannan harkoki.

Shugaba Xi ya ce, a cikin wadannan shekaru 3 da suka gabata, Sin tana daukar matakai da suka dace don bayyana yadda take ba da jagoranci ga dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya. An yi kiyasin cewa, kasar Sin dake kara bude kofa ga ketare za ta ci gaba da ba da mihimmiyar gudunmawa wajen ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kuma jagorancin dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China