Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na adawa da tsokacin Amurka kan batun Xinjiang
2019-09-19 19:35:30        cri

A yau Alhamis ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya jaddada cewa, batun jihar Xinjiang harkar cikin gidan kasar Sin ne, kuma bai kamata wata kasar waje ta tsoma baki a ciki ba, sai dai kuma a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, wasu jami'an kasar Amurka sun gaza kula da hakikanin yanayin da ake ciki, inda suke ta tsokaci maras tushe, kan manufar da kasar Sin take aiwatarwa a jihar Xinjiang, bisa dalilan kare hakkin dan Adam, matakin da kasar Sin take adawa da shi.

Jami'in ya bayyana hakan ne, yayin taron ganawa da manema labarai da aka saba yi a nan birnin Beijing, inda ya kara da cewa, batun Xinjiang ba batu ne dake shafar wata kabila ko addini, ko hakkin dan Adam ba, wato dai batu ne na yaki da ta'addanci, da hana kawo baraka ga kasa.

Kaza lika yanzu haka kasar Sin ta riga ta samu babban sakamako, yayin da take gudanar da aikin, har an kai ga yin nasarar hana aukuwar ayyukan ta'addanci a cikin shekaru 3 da suka gabata. Ya ce matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun tabbatar da ikon rayuka, da ikon zama lafiya, da ikon samun ci gaban al'ummun kabilu daban daban na kasar Sin.

Ana iya lura ma cewa, a bayyane kasar Sin ta ba da babbar gudummowa, ga aikin yaki da ta'addanci na kasa da kasa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China