Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na son hada kai da sauran kasashen duniya domin tabbatar da matsayar da aka cimma kan batun Libya
2020-01-20 19:54:27        cri

Jiya Lahadi an gudanar da taron kolin kasa da kasa kan batun Libya a birnin Berlin na kasar Jamus, yau kuma kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son hada kai tare da sauran kasashen duniya domin tabbatar da matsayar da aka cimma yayin taron, ta yadda za ta ba da gudummowarta wajen farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a kasar ta Libya.

Yayin taron ganawa da manema labaram da aka saba yi yau a nan birnin Beijing, Geng Shuang ya yi nuni da cewa, har kullum kasar Sin ta dauki matsayar adalci kan batun Libya, haka kuma tana bin ka'idojin MDD, tare kuma da nuna biyayya ga ikon mulki da 'yancin kai da cikakken yankin kasa ta kasar Libya, kana tana fatan za a daidaita rikicin Libya ta hanyar siyasa karkashin jagorancin MDD.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China