Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IOM: An kwashe kimanin bakin haure 10,000 bisa radin kansu daga Libya a 2019
2020-01-16 10:08:04        cri

Hukumar kula da kaurar jama'a ta duniya (IOM) ta bayyana a jiya Laraba cewa, ta yi nasarar kwashe kimanin bakin haure 10,000 bisa radin kansu daga Libya zuwa kasashensu na asali a shekarar 2019 da ta gabata.

Hukumar ta ce, an samu nasarar aiwatar da shirin mayar da bakin haure zuwa kasashensu na asali a shekarar 2019 ko VHR a takaice ne, bisa taimakon kungiyar tarayyar Turai da gwamnatin kasar Italiya.

Hukumar ta ce, duk da cewa, an yi ban kwana da shekarar 2019, amma za ta ci gaba da mayar da bakin haure daga Libya zuwa kasashensu na asalin bisa radin kansu.

Dubban bakin haure ne dai, gaibili 'yan Afirka, suka yi kokarin tsallaka Bahar Rum daga Libya, saboda matsalar tsaro da tashin hankali da kasar ta ke fuskanta, tun boren gama garin shekarar 2011, da ya yi awon gaba da gwamnatin marigayi shugaba Muammar Gaddafi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China