Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bakin haure 'yan Nijer 168 sun koma gida bisa radin kansu daga Libya
2019-12-14 15:05:57        cri

Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM) ta sanar a ranar Juma'a cewa, kimanin bakin haure 168 'yan jamhuriyar Nijer sun koma kasarsu ta asali bisa radin kansu daga kasar Libya.

A daren ranar Alhamis ne bakin hauren suka isa birnin Niamey ta wani jirgin saman da aka yi hayarsa tare da tallafin hukumar kula da makaurata ta kasa da kasa dake Libya, kamar yadda hukumar ta IOM ta wallafa a shafin twita.

Jami'an hukumar IOM sun tallafa wajen yin rejistar bakin hauren, da bayar da tallafin magunguna da kuma jigilar bakin hauren zuwa kasarsu.

IOM tana ci gaba da gudanar da aikin sa kai na mayar da bakin haure wadanda ke gararamba a Libya, inda take ci gaba da mayar da su zuwa kasashensu na asali.

Hukumar ta IOM ta yi kiyasin akwai bakin haure sama da 650,000 a kasar Libya a halin yanzu, daga cikin su akwai kimanin 6,000 da ake tsare da su a wasu cibiyoyi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China