Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun sojin Libya masu sansani a gabashin kasar sun musanta kai hari kan kwaleshin soji dake Tripoli
2020-01-06 09:40:38        cri

Rundunar sojojin kasar Libya mai sansani a gabashin kasar, ta ce ba ita ce ta kaddamar da hari kan kwalejin sojoji dake birnin Tripoli ba.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Benghazi na gabashin kasar, kakakin rundunar Ahmad al-Mismari, ya ce mai yiwuwa ne wani abun fashewa ne ya tarwatse, sabanin hari ta sama da ake zargin an kaiwa kwalejin.

Al-Mismari ya ce tuni aka fara gudanar da bincike a hukumance game da aukuwar lamarin, yana mai kira ga MDD da ta tura kwamitin da zai tantance gaskiyar al'amari.

Sai dai a nata bangare, gwamnatin Libya mai samun goyon bayan MDD, ta ce a ranar Asabar din karshen makon jiya, wasu dalibai su 30 sun rasu, kana wasu 33 sun jikkata, sakamakon hari ta sama da aka kai kan kwalejin horas da sojojin dake birnin Tripoli.

A ranar Lahadi kuma, ofishin jakadancin Amurka dake kasar ta Libya, ya yi Allah wadai da harin na Tripoli. Cikin wata sanarwa da ya fitar, ofishin ya yi kira ga daukacin sassan jagorancin kasar, da su kawo karshen tsoma hannun kasashen waje cikin al'amuran siyasar kasar, yana mai fatan tallafawa kasar ta kawo karshen tashe tashen hankula, da dakile ayyukan dakarun kasashen waje, da kuma sake samar da zarafin tattaunawar siyasa bisa goyon bayan MDD. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China