Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jarin Sin yana bunkasa tattalin arzikin gabashin Afrika
2020-01-15 09:41:41        cri

Wani mai sharhi kan tattalin arziki ya ce jarin da kasar Sin ke zubawa yana matukar bunkasa ci gaban tattalin arzikin shiyyar gabashin Afrika.

Judd Murigi, shugaban cibiyar nazarin tattalin arziki ta ICEA LION, ya fada a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi cewa, a yayin da saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya yi kasa, masu zuba jari daga kasar Sin suna ci gaba da neman wasu sabbin kasuwannin zuba jari dake da makomar bunkasuwa mai haske.

Murigi ya bayyana cikin mujallar ICEA LION dake nazarin tattalin arziki ta watannin uku na farkon shekarar 2020, ya ce, a shekaru biyar da suka gabata, jarin da Sinawa suka zuba shi ne babban dalilin da ya samar da bunkasuwar tattalin arzikin kasashen shiyyar gabashin Afrika fiye da sauran kasashen dake yankin kudu da hamadar Saharar Afrika.

Ya ce galibin bunkasuwar tattalin arzikin da aka samu a shiyyar gabashin Afrika ya fi shafar fannin samar da kayayyakin more rayuwar jama'a ne.

Mai sharhin ya ce, shiyyar gabashin Afrika ta yi matukar cin moriyar sabbin ayyukan gina hanyoyin mota, layin dogo, makamashi wadanda suka taimaka matuka wajen yin gogayya a fannin tattalin arziki.

Murigi ya ce jarin da Sinawa suka zuba wajen kafa rukunin masana'antu a shiyyar ya taimaka wajen bunkasa kayayyakin da ake samarwa a cikin gidan kasashen da samar da guraben aikin yi ga mazauna yankunan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China