Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akalla mutane 55 sun mutu sanadiyyar faduwar motar tanka a Niger
2019-05-07 10:54:43        cri

Hukumomi a kasar Niger sun ce, mutane akalla 55 sun mutu yayin da wasu 37 suka kone, sanadiyyar faduwar wata tankar man gas da safiyar jiya Litinin, akan babban titin shiga birnin Niamey ta bangaren gabas.

A cewar ministan harkokin cikin gida da tsaron al'umma Bozoum Mohamed, lamarin ya auku ne a lokacin da wata tankar mai da ta jirkice bayan hatsarin da ta yi, ta kama da wuta yayin da gomman mutane ke kokarin kwasar man gas din dake yoyo.

Shugaban kasar Mahamadou Issofou, da firaministan kasar Brigi Rafini da ministan lafiya Idi Illiassou Mainasara da kuma Bazoum Mohamed, sun ziyarci wadanda suka raunana dake samun kulawa a asbitocin birnin.

Gobarar ta kuma kone motoci da babura da dama. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China