Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya yi tsokaci kan dangantakar Sin da Amurka
2019-09-25 15:58:28        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci wani taron liyafa da aka gudanar a birnin New York na kasar Amurka, tare da gabatar da jawabi, wanda kwamitin dangantakar Amurka da Sin da kwamitin cinikayyar kasashen biyu da kungiyar 'yan kasuwar Amurka da kwamiti mai kula da dangantakar Amurka da kasashen ketare suka hada kai wajen shiryawa.

A cikin jawabinsa, Wang Yi ya ce, a bana ake cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin kuma ake cika shekaru 40 da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Ya ce a halin yanzu dai, dangantakar kasashen biyu na tafiyar hawainiya, kuma akwai hanyoyin biyu da za su bi, daya na da makoma mai haske, dayar na cike da wahala. Ta yaya Amurka za ta zabi hanyar da za ta bi cikin shekaru 40 masu zuwa?

A cewar Wang Yi, da farko, neman amfanin juna da cin moriya tare, hanya ce daya tilo da bangarorin biyu za su bi. Na biyu kuwa, hanyar da ta dace bangarorin biyu su bi ita ce, bude kofa da hadin kai, domin bangarorin biyu ba za su iya rabuwa da juna ba. Na uku kuma, arangama da juna zai lalata dangantakarsu, kuma ba su iya canza juna ba. Na hudu, kamata ya yi bangarorin biyu sun sauke nauyin dake wuyansu cikin hadin kai, kuma bangarorin biyu ba sai su maye gurbin juna ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China