2020-01-03 11:17:47 cri |
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bugawa takwaransa na Amurka Donald Trump waya a jiya Alhamis don tattauna halin kasashen Libiya da Sham da dai sauransu ke ciki.
Fadar shugaban Turkiya ta ba da wata sanarwa a wannan rana cewa, tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta mai da hankali sosai kan muhimmancin matakan diplomasiyya wajen warware rikicin shiyya-shiyya, tare da amince da kara hadin kansu.
A nasa bangare, Trump ya ce, yadda wasu kasashen ketare ke tsoma baki a harkokin Libya na kara dagula halin da kasar ke ciki. Ban da wannan kuma, shugabannin biyu sun yarda da sassauta halin da ake ciki a jihar Idlib don kiyaye fararen hula. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China