Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da shawarwari a sabon zagaye kan batun kasar Sham a Kazakhstan
2019-12-12 10:12:50        cri

An kammala shawarwarin Astana karo na 14 cikin kwanaki biyu, kan batun kasar Sham a jiya Laraba a Nur Sultan, fadar mulkin kasar Kazakhstan. Mahalarata taron dai sun tattauna ne kan yadda za a ci gaba da goyon bayan kwamitin tsarin mulkin Sham, da halin da ake ciki a Idlib, da kuma batun jin kai a kasar Sham da dai sauransu.

Kasashen Rasha da Turkiya da Iran, sun ba da wata hadaddiyar sanarwa ta bayan taron, inda suka bayyana cewa, kasashen uku na sa ran kara tuntubar mambobin kwamitin tsarin mulki, da manzon musamman na MDD, don ba da tabbaci ga kokarin aiwatar da harkokin kwamitin ba tare da ko wane sharadi ba. Ban da wannan kuma, kasashen uku na adawa da kowane yunkuri na kawo baraka ga cikakken yankin kasar Sham, da illata tsaron kasashen makwabtaka, da kuma kin yarda da fakewa da batun yaki da ta'addanci don samun damar da cin gashin kai ba bisa doka ba, da kuma nuna rashin jin dadi kan haramtacciyar mamaya, da kuma sayar da man fetur na kasar Sham.

Wakilan Rasha, Iran da Turkiyya da kuma Sham, da wakilan kungiyar 'yan adawa sun halarci taron, kuma a matsayin masu sa ido, wakilan gwamantocin Jordan, da Iraki, da Lebanon, da tawagar MDD suma sun halarci taron.

A gun taron, an kai ga cimma matsaya daya, cewa za a gudanar da irin wannan shawarwari a sabon zagaye a watan Maris mai zuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China