Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An ba kwamitin shirya kundin tsarin mulkin kasar Syria umarnin fara aiki
2019-09-29 17:13:54        cri
An ba kwamitin da aka kafa a Syria umarnin shirya sabon kundin tsarin mulkin kasar da yaki ya daidaita, kamar yadda jerin ka'idojin kafa kwamitin, wanda gwamnati da bangaren adawa suka amince da shi ya tanada.

Jerin ka'idojin kafa kwamitin da MDD ta fitar a jiya, ya ce akwai yiwuwar kwamitin ya sake bitar kundin tsarin mulkin kasar na 2012 da gyara kundin tsarin mulki da ake amfani da shi yanzu ko kuma sake shirya wani sabo.

Kwamitin zai kunshi sassa biyu: babba da karami, inda karamin zai kunshi mambobi 45 dake da alhakin shirya kudurorin tsarin mulki da babban sashe kwamitin mai mambobi 150 zai amince da su.

Wata sanarwa da MDD ta gabatarwa manema labarai a jiya, ta ce za a bayyana sunayen mambobi 150 na babban sashen kwamitin da zarar an tabbatar da su a hukumance.

A ranar Litinin ne Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya sanar da kafa kwamitin a hukumance. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China