Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC na Sin ya kai ziyara jamhuriyyar Congo
2019-12-14 15:55:29        cri
Bisa gayyatar da majalisar dokokin jamhuriyyar Congo ta yi masa, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC Ji Bingxuan ya kai ziyara a kasar tare da tawagarsa tun daga ranar 11 zuwa 13 ga wannan wata.

A yayin ziyararsa, Ji Bingxuan ya bayana cewa, a cikin shekaru 55 da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da jamhuriyyar Congo, kasashen biyu sun nuna girmamawa, da daidaito, da kuma sahihanci ga juna, da kuma fahimtar juna da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan da suka mayar da hankali kansu. Sin tana son yin kokari tare da jamhuriyyar Congo wajen aiwatar da ayyukan da aka tsara a gun taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito, ta hakan za a sa kaimi ga neman raya makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka。

A nata bangare, kasar jamhuriyyar Congo ta nuna godiya ga kasar Sin domin ta samar da goyon baya gare ta wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar, kana za ta kara yin mu'amala da hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannoni daban daban don amfanawa jama'arsu baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China