Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu bullar cutar Ebola karon farko, a birnin Goma na DRC
2019-07-15 10:48:28        cri

A karon farko, an tabbatar da samun bullar cutar Ebola a birnin Goma dake gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Sanarwar da ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta fitar, ta ce wani limamin Choci da ya yi mu'amala da masu cutar Ebola a garin Butembo dake arewa maso gabashin kasar ya kamu da rashin lafiya a makon da ya gabata, kuma ya shiga motar bus zuwa birnin Goma a ranar Lahadi, inda daga bisani gwaji ya tabbtar da ya kamu da cutar Ebola.

An garzaya da mutumin zuwa cibiyar kula da masu cutar Ebola. Amma ma'aikatar ta ce barazanar yaduwar cutar a birnin ba ta da yawa.

A baya-bayan nan ne hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana damuwa game da yadda Ebola ke kara yaduwa a kasar cikin 'yan watannin da suka gabata, inda mutane fiye da 2,000 suka kamu da ita tun bayan barkewarta kimanin shekara 1 da ta wuce. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China