Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane akalla 23 sun mutu sanadiyyar hadarin jirgin sama a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2019-11-25 09:47:48        cri
Akalla gawarwaki 23 aka samu a wurin da jirgin sama ya fadi a wani yanki na birnin Goma dake lardin arewacin Kivu na gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Gwamnan lardin arewacin Kivu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, jirgin mallakin kamfanin Busy Bee na kasar, ya fadi akan gidaje mintoci kalilan bayan tashinsa daga filin jirgin saman Goma, zuwa birnin Beni.

A cewar wasu majiyoyi daga ofishin gwamnan da kuma babban asibitin birnin Goma, babu wanda ya tsira daga cikin fasinjojin jirgin, ciki har da matukansa biyu.

Wasu majiyoyi dake da kusanci da kamfanin Busy Bee, sun ce an ji karar fashewar daya daga cikin injinan jirgin, mintoci kalilan bayan tashinsa. Kuma rahotanni sun ce matukin jirgin ya yi kokarin juyawa ya koma.

Jami'an filin jirgin da jami'an shirin wanzar da zaman lafiya na MDD sun yi kokarin zakulo gawarwakin wadanda suka makale a karkashin baraguzan jirgin da ya kone kurmus sanadiyyar hatsarin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China