Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fitar shirin magance matsalar tsoffi a cikin alumma
2019-11-22 10:49:51        cri

Kwamitin kolin JKS da hadin gwiwar majalisar gudanarwar kasar, sun fitar da wani shiri mai cin dogo da matsakaicin zango, dake da nufin tunkarar matsalar tsoffi a kasar.

Shirin na bukatar samar da wani managarcin tsari da zai magance matsalolin tsoffi a cikin al'umma ya zuwa 2022. Ya zuwa tsakiyar karnin, za a fara amfani da managartan tsare tsaren da za su cimma bukatun gagarumar kasar ta zamani mai hallayar gurguzu.

Shirin ya tanadi ayyukan tunkarar matsalar al'ummar tsoffi a fannoni 5.

Karkashin shirin, za a inganta tsarin raba kudin shiga na kasar da ci gaba da kara yawan ajiyar asusun fansho da kuma samar da tsarin tsaron al'umma mai dorewa da kuma tabbatar da adalci.

Har ila yau, shirin zai inganta samar da 'yan kwadago masu inganci, wanda ke bukatar kara kwarewar sabbin ma'aikata da kafa wani tsarin koyo na tsawon rai ga wadanda suka tsufa da kuma kokarin cimma samar da cikakkun ayyukan yi da kuma samar da ayyuka masu inganci.

Baya ga haka, shirin na neman samar da al'ummar da a cikinta, za a rika girmamawa tare da kulawa da tsoffi ta yadda za su yi rayuwa cikin jin dadi. Sannan za a karafafa tsarin shari'a domin kare hakkoki da muradun tsoffi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China