Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bada gudumuwar dakin nazarin fasahar sadarwa a Kenya
2019-10-28 09:56:47        cri
Jakadan kasar Sin a Kenya Wu Peng, ya gabatar da dakin nazarin fasahar sadarwa a wata makaranta dake yankin Trans-Nzoia na arewa maso yammacin Kenya, lamarin da ya sanya dalibai cikin farin ciki.

Manufar dakin da aka sanyawa kumfyutoci 45 ita ce, saukaka koyo tsakanin daliban makarantar sakandare ta Benon dake mazabar Cherangany.

Abun da aka fara yi bayan isa makarantar shi ne, shuka bishiyoyi a harabarta a matsayin alama ta kyautata muhalli.

Yayin da dalibai da iyayensu ke cikin farin, jakada Wu Peng, ya yanke kyallen dake alamta kaddamar da dakin.

Wu Peng, ya kuma jaddada muhimmancin samar da damar amfani da fasahar intanet a kauyuka domin taimakawa al'ummar kasar, musammam matasa, lalubo damarmakin ayyukan yi na dogaro da kai.

Jakadan wanda ya samu rakiyar dan majalisar yankin Joshua Kuttuny, ya yi alkawarin kafa babban dakin taro da bada gudunmuwar karin kumfyutoci domin taimakawa kauyawa samun ilimin fasahar sadarwa da kuma hada su da sauran sassan duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China