Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da taron zuba jari na nahiyar Afrika na bana a Masar
2019-11-23 16:24:55        cri

An kaddamar da karo na 4 na taron zuba jari na nahiyar Afrika na shekarar 2019, jiya Juma'a a sabuwar fadar mulkin kasar Masar.

Bikin kaddamar da taron na yini 2, ya samu halartar shugaban Masar, Abdel-Fattah al-Sisi da shugabannin gwamnatoci da kasashen Afrika da dama, tare da hamshakan 'yan kasuwa daga fadin duniya.

Da yake jawabi yayin bikin, Shugaba Abdel-Fatah al-Sisi ya ce, za a tattauna yayin taron, ta yadda za a samu ci gaba a duniya mai cike da sarkakiya da kalubale.

Ya ce kaddamar da yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci na nahiyar a ranar 30 ga watan Mayu, gagarumin ci gaba ne ga yunkurin dunkulewar nahiya, la'akari da kasancewar Afrika daya daga cikin yankunan cinikayya mafi girma a duniya dake da mutane biliyan 1.2 da tattalin arzikin da ya kai dala triliyan 2.5.

Ya ce ya kamata a samar da mafita bisa dunkulewa da sauya nahiyar zuwa cibiyar raya ayyukan masana'antu a duniya, da nufin samar da ayyukan yi ga al'ummomin nahiyar da jan hankalin masu zuba jari.

Shugaban na Masar ya kuma jaddada cewa, ci gaban nahiyar na bukatar gudunmuwar bangarori masu zaman kansu, yana mai cewa, aikin ba na gwamnatoci ne kadai ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China