Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fao: Kasar Sudan ta kudu tana fuskantar gibin tan 700,000 na abinci
2019-11-20 15:47:55        cri
Hukumar samar da abinci ta MDD (FAO) ta bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasar Sudan ta Kudu, tana fama da gibin abinci da ya kai tan dubu 700, biyo bayan ambaliyar ruwa da ta shafi sassa da dama na kasar tun a watan Yulin wannan shekara.

An yi kiyasin cewa, mutane da yawansu ya kai 908,000, ciki har da wadanda suka bar matsugunansu, da 'yan gudun hijira da al'ummomin da suka ba su wurin zama, ko dai sun rasa wuraren zamansu ko kuma ambaliyar ruwar ta shafe su, sakamakon ruwan saman da aka shatata a sassan arewacin kasar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China