Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Falasdinawa sun yaba da kuri'ar da MDD ta kada na goya musu baya
2019-11-20 10:53:37        cri
Hukumar Falasidinu, ta yi maraba da kuri'ar da MDD ta kada na goyon bayan 'yacin Falasdinawa na samun 'yancin gashin kai.

Kuri'ar ta kasance tamkar martanin gaggawa ne na kalaman da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yayi a ranar Litinin, cewa mamayar da Isra'ila ke yi a yankunan yammacin kogin Jordan bai saba dokokin kasa da kasa ba.

An rawaito ma'aikatar harkokin wajen Falasdinawa tana cewa, yayin taron kwamiti na uku na babban zauren MDD, an cimma matsayar kada kuri'a inda MDD ta gabatar da kudurin nuna goyon bayan 'yacin Falasdinawa na samun 'yancin gashin kai.

A cewar sanarwar, kimanin kuri'u 165 na mambobin kasashen ne suka goyi bayan kudurin, yayin da kuri'u 5 ne kachal suka ki amincewa, sai kuma 9 da suka kauracewa jefa kuri'ar.

Sanarwar ta kara da cewa, ministan harkokin wajen Falastinawa Riyad al-Maliki ya bukaci kasashen duniya su hada kai domin amincewa da 'yacin Falasdinawa na samun 'yancin gashin kai da kuma kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yiwa matsugunan Falastinawan.

Gagarumar kuri'ar nuna goyon bayan da aka samu kan kudurin ya nuna yadda al'ummar kasa da kasa suke nuna adawa game da matsayin da Amurka ta dauka na goyon bayan mamayar da yahudawa ke yiwa yankunan yammacin kogin Jordan. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China