Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta fitar da takardar bayani game da ci gaban mata a cikin shekaru 70
2019-09-19 16:04:23        cri
A yau ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da takardar bayani game da ci gaban da matan kasar suka samu a gwagwarmayar da suke yi a cikin shekaru 70 da suka gabata, bayan kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

Taken takadar bayanin "Daidaito, ci gaba da amfana tare: Ci gaban gwagwarmayar mata a cikin shekaru 70, bayan kafa sabuwar kasar Sin". Baya ga gabatarwa da yadda aka karkare bayanin dake kunshe cikinta, takardar ta kunshi sassa guda 9: " Muhimmancin gwagwarmayar mata da yadda ake yayata shi a kasar Sin", "Yadda rawar da mata suke takawa a fannin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a ke karuwa", "Yadda matsayin mata a fagen siyasa ya karu" da "Yadda matsayin mata a fagen Ilimi ya karu nesa ba kusa ba", da "Yadda yanayin lafiyar mata ya karu sosai", da "Yadda yanayin tsaron mata ke ci gaba da karuwa", da "Yadda mata ke taka rawa a harkokin gina iyali", da "Yadda ake damawa da mata a ayyukan musaya da hadin gwiwa na kasa da kasa". (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China