Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta dauki matakan samar da amfanin gona da daidaita farashi
2019-11-08 11:16:04        cri
Gwamnatin kasar Sin ta bayyana kudurinta na daukar kwararan matakan tabbatar da samar da muhimman kayan amfanin gona da ma daidaita farashin kaya.

Majalisar gudanarwar kasar ce ta yanke wannan shekara, yayin zamanta na ranar Laraba da firaministan kasar Li Keqiang ya jagoranta.

Taron ya kuma yi kira da a kara zage dantse don kare gonaki, da kara yawa da ma ingancin hatsin da ake samarwa, ta yadda za a samu nasarar girbin amfani gona a wannan kakar da ma lokacin hunturu.

Haka kuma taron, ya yanke shawarar daukar matakan noma manyan gonaki, don kara samun amfanin gona. Manufar ita ce, raya eka miliyan 67 na irin wadannan gonaki nan da shekarar 2020, inda ake fatan samun sama da ta kilogram biliyan 500 na amfanin gona.

Firaminista Li ya ce, ya kamata a samarwa masu wadanda kudin shigarsu bai taka kara ya karya ba a fadin kasar rangwamen farashi, ta yadda rayuwar su za ta inganta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China