Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar AfCFTA ba za ta kawo tasiri ga haraji ba, in ji hukumar kwastam
2019-11-07 09:26:47        cri

Hukumar kwastam ta duniya a shiyyar gabashi da kudancin Afrika a ranar Laraba ta kawar da duk wata fargaba game da batun karbar kudaden haraji a tsakanin kasashen Afrika, da zarar yarjejeniyar ciniki maras shinge ta AfCFTA ta fara aiki.

Larry Liza, daraktan hukumar kwastom mai kula da sashen bunkasa ci gaba, ya ce, ya kamata kasashen su hada kansu wajen daukar matakan aiwatar da yarjejeniyar da tsara dokokin da za su tabbatar da ba da kariya wajen karbar kudaden haraji a mu'amalar cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.

Ya ce akwai bukatar kasashen su yi nazari game da irin alfanun da ake tsammanin samu karkashin yarjejeniyar.

Kamfanin dillancin labarai mallakar kasar Zambiya ZANIS ya rawaito jami'in yana cewa, akwai yiwuwar yanayin kasuwanci zai iya shafar biyan kudin haraji, to sai dai yarjejeniyar ta fi alfanu matuka ga al'umma sakamakon yadda za ta kara bunkasa harkokin cinikayya da samar da damammakin kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar.

A cewarsa, bai kamata masu ruwa da tsaki su nuna shakku game da aiwatar da yarjejeniyar ba, ya kara da cewa, za ta ba da dama ga al'ummomin shiyyar su samu damar shiga kasuwannin kasashen ketare.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China