Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan sabbin kasashen da za su halarci bikin CIIE a wannan karo ya zarce kashi daya cikin uku bisa adadin kasashe masu halarta
2019-11-02 19:12:17        cri

Za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin wato CIIE karo na 2,daga ranar 5 zuwa 10 ga wannan wata a birnin Shanghai dake kasar Sin. Yawan kasashe manyan baki da za su halarci bikin CIIE a wannan karo ya karu daga 12 zuwa 15 bisa na karon da ya gabata, kana yawan sabbin kasashen da za su halarci bikin ya zarce kashi daya cikin uku na adadin kasashe 64 masu halarta a wannan karo. Fadin yankin nune-nunen kamfanonin Amurka, da Japan, da Jamus, da yankin Hong Kong na kasar Sin, da Koriya ta Kudu, su ne a matsayi na kan gaba a wannan karo, kana kasashe 40 masu rangwamen ci gaba za su halarci bikin nune-nunen kamfanoni, inda za a samar da shaguna biyu kyauta ga kowacce daga cikin kasashen 40.

Idan aka kwatanta da bikin CIIE karo na farko, yawan kasashe manyan baki da za su halarci bikin karo na biyu ya karu sosai, kuma salon dakunan nune-nunen bikin ya bambanta sosai. A gun taron manema labaru da aka gudanar a yau, mai taimakawa ministan ciniki na kasar Sin kuma mataimakin darektan ofishin shirya bikin CIIE Ren Hongbin ya yi bayanin cewa, yawan kasashe manyan baki da za su halarci bikin CIIE a wannan karo ya karu daga 12 zuwa 15 bisa yawansu a karo na farko. Yawan sabbin kasashen da za su halarci bikin ya zarce kashi daya cikin uku na adadin kasashe masu halarta. A cikin kasashe 64 da kungiyoyin kasa da kasa 3 masu halarta a wannan karo, baya ga kasar Sin, wannan ne karo na farko da kasashe 24 za su halarci bikin, sannan wannan ne karo na 2 da kasashe 39 za su halarci bikin, wadanda suka zo daga nahiyoyi 5 a duniya. Kana ana da salo iri iri na dakunan nune-nunen bikin. Kasa da kasa za su yi amfani da fasahohin gargajiya da na zamani don shaida fifikonsu a fannonin cinikin kaya, da samar da hidima, da zuba jari, da yawon shakatawa, da al'adu, da kimiyya da fasaha da sauransu.

Bayan da aka gama bikin CIIE a wannan karo, dakunan nune-nunen kasashe 64 za su ci gaba da gwada nune-nune har na tsawon kwanaki 8, ana sa ran cewa, za a biya bukatun masu kallo dubu 400 da za su kai ziyara.

Bikin nune-nunen kamfanoni ya fi jan hankalin jama'a. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, fadin nune-nunen kamfanonin kasashen Amurka, da Japan, da Jamus, da yankin Hong Kong na kasar Sin, da Koriya ta Kudu, da Italiya, da Faransa, da Australia, da Switzerland, da kuma Birtaniya na cikin matsayi 10 na kan gaba a bikin. Matsakaicin fadin wurin nune-nunen kamfanoni da yawan kamfanonin da za su yin adon musamman a bikin ya karu sosai bisa na karon da ya gabata. Malam Ren Hongbin ya yi bayani game da manufofin samar da sauki don nuna goyon baya ga kasashe mafi rashin ci gaba da za su halarci bikin a wannan karo. Ya ce, don sa kaimi ga kasashe mafi rashin ci gaba da su halarci bikin CIIE, da cimma burin raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, da more fasahohin bunkasuwar kasar Sin, yawan kasashe mafi rashin ci gaba da za su halarci bikin CIIE a wannan karo ya kai 40. Kana za a samar da shaguna biyu kyauta ga kowanensu.

Bayan kammala bikin CIIE karo na biyu, wasu kayayyakin nune-nunen za su shiga cibiyar cinikin kayayyaki da ake shigowa da su kasar Sin ta Hongqiao da kuma cibiyar cinikayya ta duniya ta Greenland, inda jama'a za su iya sayen su, ta hakan za a hada aikin nune-nunen kayayyaki da aikin sayarwa tare.

A yayin bikin CIIE karo na biyu, za a ci gaba da gudanar da dandalin tattauna batutuwan tattalin arzikin kasa da kasa na Hongqiao, inda za a tattauna batutuwan yanayin ciniki, da fasahar AI, da yin kwaskwarima kan hukumar ciniki ta duniya, da ciniki ta yanar gizo, raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama da sauransu.

Mataimakin sashen kula da harkokin kasa da kasa na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Chen Chao ya bayyanawa 'yan jarida cewa, za a shaida imani na raya kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon baya ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya da kuma tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban a gun dandalin tattaunawar. Ya ce, a gun dandalin tattaunawar, za a gudanar da wasu bukukuwa na musamman tare da wasu kungiyoyin kasa da kasa da wasu manyan kungiyoyin masana na duniya, da gabatar da rahotannin nazari da litattafan da abin ya shafa. Kana za a rubuta ra'ayoyin masu ba da jawabi a gun dandalin tattaunawar, da tattauna yanayin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, tare da yin bayani game da manufofin Sin na yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, ta hakan za a maida dandalin tattaunawar a matsayin muhimmin dandalin gabatar da manufofin sarrafa tattalin arzikin duniya da na bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China