Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na fatan karfafa hadin kai tare da kasashen duniya ta hanyar CIIE
2019-11-01 15:37:01        cri

A yayin taron manema labaru da aka shirya a ranar 30 ga watan da ya wuce a birnin Alkahiran kasar Masar, jakadan kasar Sin dake kasar, Liao Liqiang, ya bayyana yadda ake share fagen bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) karo na biyu, inda ya ce, bikin baje kolin zai nace ga manufar gudanar da harkokin duniya irin na yin shawarwari tare kan manyan manufofin hadin kai, da kafa dandalin hadin kai tare, da kuma more nasarorin da aka cimma, da nufin kasancewa wani dandamali mai bude kofa na kasashe daban daban wajen karfafa hadin kai da mu'amala, da kuma gudanar da cinikayyar kasa da kasa.

A wannan rana, akwai muhimman kafofin watsa labaru na kasar Masar sama da goma da suka halarci taron manema labarun, inda da farko jakada Liao ya yi bayani kan yanayin bikin baje kolin na CIIE na wannan karo.

"Za a shirya bikin baje kolin CIIE karo na biyu ne a tsakanin ranekun 5 zuwa 10 ga wata a cibiyar baje kolin kasa ta Shanghai, a waje guda kuma za a shirya wani dandalin tattauna harkokin tattalin arzikin kasa da kasa, wato dandalin tattaunawa na Hongqiao. Ya zuwa yanzu, akwai kasashe 64 da za su halarci bikin nune-nune na kasashe, game da bikin nune-nunen kamfanoni, kuma za a hada da kayayyakin cinikayya, fasahohi da kuma hidima, wadanda ke shafar kimiyya da fasaha, motoci, na'urori, kayayyakin aikin jinya da harkokin kiwon lafiya, harkokin jin dadin zaman rayuwa, cinikin ba da hidima, abinci da kuma amfanin gona, wadanda za a nuna su a yankunan nune-nune guda bakwai."

Jakada Liao ya nuna cewa, idan aka kwatanta shi da na farko, bikin baje kolin na wannan karo yana da halin musamman na mafi kasaita da inganci.

"Akwai kamfanoni sama da 3000 da 'yan kasuwa sama da dubu 400 da suka yi rajistar shiga bikin baje kolin, wanda ya fi tasiri bisa na bara, ban da wannan kuma, kamfanonin dake cikin jerin fitattun kamfanoni guda 500 na kasa da kasa da manyan fannoni a sana'o'insu da suka tabbatar da halartar bikin baje kolin sun fi yawa bisa na baya, kana kuma akwai wasu matsakaita da kananan kamfanoni da dama dake matsayin gaba a kasashen duniya."

Jakada Liao ya kara bayyana cewa, kamfanonin da za su halarci bikin baje kolin na wannan karo sun fi karfi a fannonin sana'o'insu, kamfanonin dake cikin jerin fitattun kamfanoni guda 500 na kasa da kasa da manyan fannoni a sana'o'insu da za su halarci bikin baje kolin sun fi yawa bisa na bara, kason masu kallon da masu sayen kayayyaki na kasa da kasa shi ma ya karu. Ban da wannan kuma, ingancin kayayyaki da kwarewa da yadda suka yi daidai da zamani da halinsu na musammam ya karu sosai, dukkansu na kokarin wakiltar babban matsayin da kasashensu ke dauka a fannoni daban daban. Haka zalika, bakin da za su ba da jawabi a dandalin tattaunawa da mahalarta bikin sun fi na bara yawa da kuma karfin fada a ji. Game da batutuwan da za a tattauna a dandalin kuma, yawancinsu za su mai da hankali kan dunkulewar tattalin arzikin duniya, da raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa, da hangen nesa da kuma kara kwarewa.

A matsayinta na wata babbar kasa mai tasowa a duniyar Larabawa da nahiyar Afirka, gwamnati da masu masana'antu da 'yan kasuwar kasar Masar dukkansu suna nuna sha'awa sosai kan bikin baje kolin na CIIE. A shekarar 2018, firaministan kasar Mostafa Madbouly ya jagoranci tawagar wakilan gwamnati don halartar bikin baje kolin na farko. Bayan shawarwarin da aka yi, kamfanoni mahalarta bikin da masu sayen kayayyakin sun cimma yarjeniyoyin kasuwanci dake shafar dala Amurka miliyan 42. Jakada Liao ya ce, bikin baje kolin na bana, shi ma ya samu amsa sosai daga wajen gwamnati da kamfanonin kasar Masar. Ya zuwa yanzu, kamfanonin kasar da suka yi rajistar halartar bikin sun kai 23. A cewar jakada Liao,

"Ina fatan yin amfani da dandamalin na bikin baje kolin na CIIE don taimakawa duniya kara fahimtar kasar Masar da kuma son kasar. Baya ga haka kuma, ina fatan amfani da wannan dama mai kyau, don karfafa huldar dake tsakanin jama'ar Sin da Masar."

Jakada Liao ya jaddada cewa, shirya bikin baje kolin na CIIE da kasar Sin za ta yi ya nuna matsayinta na tsayawa ra'ayin moriya na daidaito, da kokarin da take yi wajen bunkasa ci gaban duniya, wanda ya haifar da fatan samun makoma mai kyau ga duk duniya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China