Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Faransa na fatan karfafa alaka da kamfanonin kasar Sin ta hanyar halartar bikin CIIE
2019-10-31 11:27:00        cri


Za'a yi bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu ko kuma CIIE a takaice daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwambar bana a birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, inda Faransa ta zama daya daga cikin wasu muhimman kasashe 15 wadanda kasar Sin ta zabo don su bayyana al'adunsu na musamman a wajen bikin. Hukumar bunkasa harkokin kasuwanci ta babban yankin Provence na kasar Faransa ta ce, tana fatan amfani da damar halartar bikin CIIE don kara inganta alaka tare da kamfanonin kasar Sin.

Babban yankin Aix-Marseille-Provence na kasar Faransa babbar mahada ce a nahiyar Turai ta harkokin sadarwar kasa da kasa. Shugaban hukumar bunkasa kasuwanci ta yankin Philippe Stefanini ya bayyana cewa, yankin Aix-Marseille-Provence na da matukar muhimmanci, musamman ta fuskar inganta mu'amalar cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Turai da Afirka. Ya kara da cewa, yana fatan hukumarsa za ta inganta dangantakar kut da kut da kamfanonin hadin-gwiwa na kasar Sin ta hanyar halartar bikin CIIE a wannan shekara, inda ya ce:

"Wannan muhimmiyar dama ce gare mu. Bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ya samarwa kamfanonin Faransa wani babban dandali na inganta hadin-gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin. A bara, mun kulla alaka da kamfanonin kasar Sin a fannonin da suka shafi kayan kwalliya da motoci masu amfani da karfin wutar lantarki da makamashi da sauransu. A bana kuma mun yanke shawarar ci gaba da halartar bikin CIIE a karo na biyu, don yin mu'amala da kamfanonin kasar Sin da suke sha'awar yin kasuwanci a Faransa."

Kamfanin kera injunan jirage na kasa da kasa mai suna Weichai Power Baudouin na daya daga cikin kyawawan misalan dake shaida irin hadin-gwiwar dake kasancewa tsakanin Sin da Faransa. A shekara ta 2009, kamfanin Weichai na kasar Sin ya sayi kamfanin kera injunan jiragen ruwa na kasar Faransa mai suna Baudouin mai dogon tarihi, wanda ya fice daga mawuyacin halin da yake ciki har yana samun farfadowa cikin sauri. A bana, kamfanin Baudouin shi ma zai je Shanghai don halatar bikin CIIE. A nasa bangaren, mataimakin shugaban kamfanin Baudouin Emmanuelle Tellier ya ce, bikin CIIE ya shaida niyyar kasar Sin ta fadada bude kofarta ga kasashen waje, kuma kamfaninsa na fatan bude kasuwannin injunan jiragen ruwa a kasar Sin. Mista Emmanuelle ya nuna cewa:

"Duk wani kamfani wanda yake son habaka kasuwanci, har ya zama babban kamfani a duniya, ya zama dole ya samu bunkasuwa a kasar Sin, wadda ke da kasuwa mafi girma a duk fadin duniya. Kasar Sin za ta samar da dimbin damammaki ga kamfanin Weichai da kamfaninmu na Baudouin. Tallata kayanmu a kasuwar kasar Sin bisa taimakon kamfanin Weichai na kasar Sin na da muhimmanci sosai, kana bikin CIIE shi ma ya samar mana da wani muhimmin dandali."

A 'yan shekarun nan, babban yankin Aix-Marseille-Provence na kasar Faransa na maida hankali sosai wajen inganta hadin-gwiwa da mu'amala tare da kasar Sin a bangarorin tattalin arziki, da cinikayya, da yawon bude ido, da muhimman ababen more rayuwar al'umma. Shugaban kungiyar kula da harkokin masana'antu da kasuwanci na yankin, Mista Jean Luc Chauvin ya ce, manufar ci gaban yankin na mai da hankali kan kafa wata dadaddiyar alakar hadin-gwiwa da kasar Sin, don haka suna dora muhimmanci sosai kan inganta hadin-gwiwa ta fannin bada ilimi. Mista Chauvin ya bayyana cewa:

"Burinmu shi ne ba kawai mu jawo hankalin shugabannin kamfanoni da masu zuba jari ba ne kadai, har ma muna dukufa kan kulla dangantaka da matasa masu ilimi na kasar Sin. Muna fatan matasanmu da wadanda za su zama shugabannin manyan kamfanonin kasarmu, za su kara samun fahimtar juna ta fannin al'adu, ta yadda za mu kafa dangantaka ga kamfanoninmu na nan gaba."

A halin yanzu, babbar kwalejin ilimin kasuwanci ta Kedge dake birnin Marseille wadda ta yi suna sosai a nahiyar Turai tana gudanar da hadin-gwiwa tare da jami'o'in kasar Sin da dama, har ta kafa rashenta a birnin Suzhou na kasar Sin, wanda ya karbi daliban kasar Sin sama da dari 8 a kowace shekara.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China