Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ingancin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin na karuwa
2019-10-21 19:50:39        cri
A yayin da ake fuskantar yanayin tabarbarewar tattalin arzikin duniya, saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu, amma duk da haka yana gudana yadda ya kamata. Don haka, kasar Sin na cike da imani, kuma tana da kwarewar cimma burin da ta tsara game da ci gaban tattalin arziki bisa manyan fannoni. Idan aka kalli ma'aunan tattalin arziki daban daban, za a gano cewa, idan an kara samar da guraban ayyukan yi, kara kudin shiga na mazauna kasar, kyautata muhallin halittu, da kara ingancin ci gaban tattalin arziki, to saurin ci gaban tattalin arzikin kasar ba zai gamu da matsalar tangal-tangal ba. Wadannan sune dalilan da suka sanya kasashen duniya su yi imani da makomar tattalin arzikin kasar Sin.

Bai kamata a duba yanayin da ake ciki yanzu ba kawai, a maimakon haka, kamata a yi hangen nesa. A yanzu haka tsarin tattalin arzikin kasar Sin da zaman rayuwar jama'arta duk suna kara kyautatuwa, kana bunkasuwar tattalin arzikin kasar shi ma yana inganci, ana iya cewa, hali mai kyau da tattalin arzikin kasar Sin ya dade yana ciki, bai sauya ba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China