Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na da kwarewar cimma muradun bunkasawar tattalin arziki a manyan fannoni
2019-10-19 15:44:23        cri

 

A yau Asabar, babban rukunin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin CMG, ya fitar da wani bayani mai taken "Sin na da kwarewar cimma muradun bunkasar tattalin arziki a manyan fannoni", wanda ya nuna cewa, a wurin taron masana'antu kan fasahar VR na shekarar 2019 da aka yi a yau din, mataimakin firaministan kasar Sin Liu He ya gabatar da jawabi. Matakin da ya kunshi sakonni masu yakini guda uku. Da farko dai, tattalin arzikin Sin na da makoma mai haske. Na biyu, Sin da Amurka na samun ci gaba mai armashi a fannoni da dama cikin shawarwarinsu, abin da ya ayyana tushe mai inganci wajen kulla wata yarjejeniya a mataki-mataki. Na uku kuma, Sin na da imanin cimma muradun bunkasar tattalin arziki a manyan fannoni. Rahotanni na cewa, GDPn farkon watanni 9 da suka gabata na bana ya karu zuwa kashi 6.2 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, adadin da ya fi sauri a duniya, wanda kuma ya bayyana kwarewar da Sin ke da ita wajen samun ci gaba mai dorewa da tinkarar kalubale, da kuma karfin gwamnatin kasar Sin na amfani da manufofi da tsare-tsare.

Game da takaddamar Sin da Amurka kuwa, bayani ya jaddada cewa, dakatar da wannan rikici zai amfanawa kasashen biyu baki daya, har ma da taimakawa duk duniya, wanda ya kasance matsaya daya da kasashen biyu suka cimma a shawarwarinsu. Bayanin ya kara da cewa, Sin na da kwazo da isashen karfin masu sayayya da masu samar da kayayyaki, kuma tana da karfin tinkarar mawuyancin hali, da kuma nagartattun manufofi a manyan fannoni, matakan da ya sa take da kwarin gwiwar tinkarar ko wani irin kalubale, don tabbatar da cimma muradun bunkasar tattalin arziki a wasu manyan fannoni da ingiza ci gaba mai inganci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China