Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadarin kwale-kwale ya halaka mutane 38 a yankin arewa maso gabashin Najeriya
2019-10-09 19:21:59        cri
Hadarin kwale-kwale ya halaka mutane 38 a yankin arewa maso gabashin Najeriya

Rahotanni daga jihar Bauchi, a yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa, mutane 38 sun gamu da ajalinsu a farkon wannan mako, lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kifi a kusa da kauyen Kuna dake karamar hukumar Kirfi.

Shugaban karamar hukumar Kirfi Bappa Abdu Bara, ya shaidawa manema labarai a garin Bauchi cewa, wadanda hadarin ya rutsa da su, manoma ne, dake kokarin zuwa gonakinsu a cikin kwale-kwale, lokacin da hadarin ya faru.

Bayanai na cewa, mutane 40 ne a cikin kwale-kwalen lokacin da hadarin ya faru, amma mutane biyu kawai aka ceto.

Rundunar 'yan sanda da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Bauchi, sun bayyana cewa, an fara gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa kifewar kwale-kwalen.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana lamarin cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe, a matsayin mai tayar da hankali, ba ma ga iyalan wadanda lamarin ya shafa ba, amma har ma ga kasa baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China