Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kalla mayakan Boko Haram 20 ne suka mika wuya ga sojojin Najeriya
2019-10-10 19:09:36        cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mayakan Boko Haram 20 ne suka mika wuya ga dakarun kasar, biyo bayan jerin hare-hare da suka kaddamar a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

Shugaban kungiyar 'yan kato da goro ta jihar Borno (CJTF) Bashir kaka, ya bayyana cewa, 15 daga cikinsu sun mika makamansu a lokacin da sojoji da 'yan kato da goran suka kaddamar da hari a kauyen Pulka dake yankin karamar hukumar Gwoza na jihar Borno.

Kaka, ya ce wasu daga cikin jagororin mayakan na Boko Haram da suka mika wuya a lokacin kai harin na ranar Laraba, na daga cikin wadanda tun farko sojojin ke nema ruwa a jallo.

Mai magana da yawun sojojin Najeriyar dake jihar Borno Aminu Iliyasu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu karin 'yan kungiyar Boko Haram biyar sun mika wuya ga sojoji a yankunan kananan hukumomin Gamboru Ngala da Dikwa dake jihar ta Borno, yayin irin wadannan hare-hare da jami'an tsaron suka kaddamar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China