Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana adawa da matakan wasu Amurkawa kan alakar BRI
2019-08-28 19:42:30        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana cewa, kasarsa tana adawa da matakan wasu mutane a Amurka na kokarin gurgunta hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya, da ma neman kulla alaka da wasu kasashe.

Geng ya bayyana hakan ne, yayin da yake mayar da martani kan rahotannin dake cewa, mashawarcin tsaron Amurka John Bolton ya shaidawa manema labarai kafin ziyarar da zai kai Ukraine cewa, kasar Sin tana kokarin fadada tattalin arzikin duniya ta hanyar shawarar ziri daya da hanya daya, da ma duk wani mataki na janyo masu zuba jari. Inda ya ce, zai gargadi Amurkawa abokansu da sauran abokan hulda game da hadarin dake tattare da jarin kasar Sin.

Sai dai a martanin da ya mayar, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana hada kai da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 160, ciki har da kasar Ukraine, don gina shawarar ziri daya da hanya daya, kuma har kullum tana martaba akidar tuntubar juna, da gudummawar hadin gwiwa da cin moriya tare.

Kasar Sin ta yi imanin cewa, galibin kasashe a duniya, za su tsara manufofinsu da kansu, ta yadda za su dace da yanayin da suke ciki da burin da suke fatan cimmawa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China