Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ajandar AfCFTA na bukatar jarin Sin kan kayayyakin more rayuwa
2019-07-10 09:46:33        cri

Wani masanin harkokin tattalin arziki na kasar Ghana, Said Boakye, ya ce idan ana son cimma burin yankin ciniki mara shinge na Afrika, akwai bukatar kasar Sin ta taimaka wajen gina ababen more rayuwa da ake bukata domin cinikayya a nahiyar.

Said Boakye, babban jami'in bincike a cibiyar nazarin harkokin tattalin arziki ta IFS, dake kan gaba wajen tsara manufofi a Ghana, ya ce daga karshe, ita ma kasar Sin za ta amfana daga fadadar tattalin arzikin nahiyar dake da ingantacciyar dangantakar cinikayya da ita.

Ya kuma yabawa manufar yankin ciniki mara shinge na nahiyar saboda zai samar da moriyar juna tsakanin masu sarrafa kayayyaki da masu sayyayya.

Jami'in ya ce, a nan gaba, idan cinikayya ta taimakawa kasashen Afrika samun ci gaba cikin sauri, za ta iya bunkasa cinikayyar da kasar Sin, saboda yanzu kasashen Afrika za su samu ci gaban da zai kai su ga sayayyar a wajen nahiyar.

Ya ce, karuwar cinikayya tsakanin kasashen Afrika, za ta fadada tattalin arzikin nahiyar, wanda kuma zai taimaka ga inganta cinikayya tsakaninta da kasashe kamar Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China