Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gidan namun daji na Shanghai zai nuna nau'o'in halittun Afirka dake bacewa daga doron kasa
2019-09-24 10:00:28        cri

Gidauniyar kare namun daji ta Afirka dake birnin Nairobin Kenya (AWF) za ta hada gwiwa da gidan adana namun daji na Shanghai na kasar Sin, inda za su shafe watanni biyu suna nune-nunen wasu nau'o'in dabbobin Afirka dake fuskantar barazanar bacewa.

Taken shirin wanda za a fara ranar Asabar mai zuwa shi ne, "kare nau'o'in dabbobin Afirka dake fuskantar barazanar bacewa".

Da take karin haske cikin wata sanarwa, gidauniyar ta AWF ta bayyana cewa, yayin nune-nunen wanda zai fara daga ranar 28 ga watan Satumba zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba a gidan adana namun daji na Shanghai, za a nuna hotunan nau'o'in halittu na Afirka dake fuskantar barazanar bacewa da kuma kokarin da ake na kare su.

Ana kuma sa ran nune-nunen za su janyo dubban masu ziyara, a wani bangare na ilimantar da jama'a game da yaki da cinikin sassan namun daji a Afirka ba bisa ka'ida.

Gidauniyar ta kara da cewa, za a gudanar da nune-nunen ne, a daidai gabar da kasar Sin ke tantance gajerun fina-finan da za su lashe lambar yabo ta "Abin da ke faruwa a yankin kahon Afirka", fim na farko dake bayyana labarin yaki da masu farauta a Afirka daga bangarori na waje. An dai shirya fim din ne, bisa abubuwan dake faruwa a zahiri.

AWF dai ta hada gwiwa da hukumomin kasar Sin, wajen kara ilimantar da jama'a game da barazanar da muhimman nau'o'in halittu na Afirka kamar giwaye da dabbobi masu shayarwa ke fuskanta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China